Mayakan kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun yi luguden wuta da makamai igwa a kan sansanin sojojin HKI a kan tuddan Kafar shuba na kasar Lebanon da take mamaye da shi.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto wani bayanin da kungiyar ta fitar a jiya litinin, yana cewa mayakan kungiyar sun yi amfani da makaman igwa a hare haren da suka kaiwa sansanin sojojin HKI mai suna ‘Rawisaat Al-alam’ da ke kan tuddan kafar shuba.
Bayanin ya kara da cewa sun kai wadannan hare hare ne don tallafawa al-ummar Falasdinu wacce sojojin HKI suke zalunta a zirin gaza. Sannan tare da maida martini dangane da hare haren da sojojin HK suke kaiwa kan wasu yankunan a kudancin kasar ta Lebanon.
Bayanin ya kara da cewa dakareun na Hizbullah, har’ila yau sun kai hare hare kan wani sansanin sojojin HKI a garin ‘Arabul Araamisha dake cikin arewacin falasdinu da aka mamaye.
A wani labarin kuma Khakham Abiishayi Livi , wani babban malamin yahudawan sahyoniyya ya bayyana cewa hare haren da kungiyar Hizbullah take kaiwa kan arewacin Falasdinu da aka mamaye, yana da tsanani , sannan yahudawan basu taba ganin irinsu bat un bayan kafuwar haramtacciyar kasar a shekara 1948.
Livi ya kara da cewa a karon farko tun bayan kafuwar HKI a shekara 1948, ba’a gudanar da bukukuwan “Fash” a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye ba. Saboda hare haren na kungiyar Hizbullah. Wasu kafafen yada labaran yahudawan sun bayyana cewa a jiya litinin kadai makamai masu linzami akalla 40 ne suka fada a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye. Sannan wasu kuma sun bayyana cewa a araewcin birnin Jalil kadai makamai masu linzami 15 suke fada a yankin daga kudancin kasar Lebanon.