A yayin gangamin daliban na jami’ar San’anti ta Iran sun kuma yi tir da kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falaasdinu,musamman ma dai a yankin Gaza.
Gabanin wannan lokacin daliban na jami’oin Iran da kuma malamansu sun gudanar da taruka inda su ka nuna cikakken goyon bayansu ga al’ummar Falasdinu da ake zalunta.
A can kasar Amurka jami’oin kasar kusan 100 ne su ka shiga cikin jerin masu adawa da yadda kasarsu take bai wa HKI goyon baya alhali tana yi wa Falasdinawa kisan kare dangi.
Sai dai wasu rahotannin da suke fitowa daga Amurkan suna nuni cewa jami’an tsaron kasar sun yi kutse a cikin harabar jami’an Columbia domin tarwatsa daliban masu zaman dirshen.
Baya ga kasar Amurka, a cikin kasashen turai da dama ma ana gudanar da Zanga-zangar nuna goyon Falisdawa, da yin tir da kisan iyashin da HKI take yi musu.