Search
Close this search box.

Iran Ta Fara Tattaunawa Da Bankin Raya Kasashen Musulmi Don Samun Kudaden Aiwatar Da Manya Manyan Ayyuka 3 A Kasar

 Bankin raya kasashen Musulmi (IDB) ya fara tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Iran a birnin Riyad na kasar Saudiya, don samar da kudade wadanda zata

 Bankin raya kasashen Musulmi (IDB) ya fara tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar Iran a birnin Riyad na kasar Saudiya, don samar da kudade wadanda zata yi amfani da su don aiwatar da manya manyan ayyuka a kasar.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Sayyid Ehsan Khonduzi, ministan tattalin arzi da kudi na JMI  yana fadar haka a gefen taron bankin IDB da ke gudana a birnin Riyad.

Ya kuma kara da cewa, tun bayan takunkuman tattalin arzikin masu tsanani wadanda  kasashen yamma suka dorawa JMI, bankin IDB ne kawai yake taimakawa kasarsa da kudade.

Ministan ya kamala da cewa a halin yanzun gwamnatin JMI tana bukatar bankin ya kara bada kudade don aiwatar da wasu Karin  manya manyan ayyuka har guda uku, da suka shafi kiwon lafiya da tsabta, wanda kuma  kari ne  a kan kudaden da ta bawa kasar don aiwatar da wasu ayyuka guda 11.

Bankin Islamic Development Bank  ko IDF, shi ne cibiyar kudade mafi girma na kasashen musulmi 57. Kuma yakan basu kudade don aiwatar da manya manyan ayyuyka a kasashen .

 

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments