Search
Close this search box.

An Kori Jakadan Kasar Jamus Daga Jami’a A Yammacin Kogin Jordan

Daliban Falasdinawa sun kori jakadan kasar Jamus daga jami’ar “ Brzint”dake Ramallah a yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda gwamnatin kasarsa take

Daliban Falasdinawa sun kori jakadan kasar Jamus daga jami’ar “ Brzint”dake Ramallah a yammacin kogin Jordan saboda nuna kin amincewa da yadda gwamnatin kasarsa take goyon bayan HKI.

A halin yanzu a duniya ana kara samun masu nuna adawa da kasashen da suke nuna goyon bayana HKI a yakin kisan kiyashi da take yi wa al’ummar Falasdinu,musamman mutanen Gaza.

Kasar Jamus  tana cikin kasashen da su ka fi zakalkalewa wajen marawa HKi goyon baya a kisan kiyashin da take yi a Faalsdinu.

Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawa da su ka yi shahada sanadiyyar kisan da HKi take yi musu sun haura 34,000 da 535,yayin da wadan da su ka jikkata kuwa su ka haura 77,000 da 704.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments