Kasashen Iran Da Zimbabwe Sun Jaddada Karfafa Alaka A Tsakaninsu

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya gana da takwaransa na Zimbabwe a birnin Geneva na kasar Switzerland Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Mohammad

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya gana da takwaransa na Zimbabwe a birnin Geneva na kasar Switzerland

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran, Mohammad Baqir Qalibaf, ya gana da takwaransa na kasar Zimbabwe Jacob Mudenda, inda suka yi musayar ra’ayi kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma batutuwa daban-daban na kasa da kasa.

Shugabannin Majalisun kasashen biyu sun gana ne a gefen zaman taron kungiyar Majalisun kasashen duniya karo na 149 da aka yi a birnin Geneva.

Taron shugabannin Majalisun kasashen Duniya karo na 149 na kungiyar ‘yan Majalisun Dokokin kasa da kasa ya bayyana batun amfani da kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire don samun zaman lafiya mafi dorewar a makomar kasashe.

An kafa kungiyar Inter-Parliamentary Union (IPU) da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya ce a shekara ta 1889, kuma babban burinta shi ne inganta zaman lafiya da hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattaunawa tsakanin Majalisun Dokokin Duniya, inda ake gudanar da manyan zaman tarukan koli guda biyu a duk shekara kuma shugabannin Majalisun Dokoki da sauran wakilan Majalisu kasashen duniya ke gudanar da zaman tattaunawa tare da musayar ra’ayoyi da  amincewa da wasu kudurori da za su amfani duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments