Kasashen Iran Da Venuzuwela Sun Yi Tir Da Matakin Da Amurka Ta Dauka A Yankin Karebiya

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi  da takwaransa na venuzuwela  Van gil Pinto sun tattauna ta wayar tarho inda suka yi tir da kasancewar

Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi  da takwaransa na venuzuwela  Van gil Pinto sun tattauna ta wayar tarho inda suka yi tir da kasancewar sojojin  Amurka a yankin karebiya, yace hakan ya sabama dokokin kasa da kasa, kuma sun jaddada matsayinsu na kara karfafa dangantakar dake tsakani da kuma yin aiki tare.

Kasancewar sojojin Amurka a yankin karebiya ya haifar da fargaba sosai, inda venzuwela ta zargi Amurka da kawo cikas a tsaron teku, da kuma keta alfarma kasarta, don  haka tattaunawar ta bayyana irin hadin kai dake tsakanin iran da kuma venuzuwela wajen kalubalantar tasirin Amurka .

Ana sa bangaren ministan harkokin wajen Venuzuwela ya jinjinawa kasar iran game da goyon bayan da take bata, ya jaddada matsayinta na kare martabar kasar da yancinta kan matsin lambar Amurka, dukkan ministocin sun amince da bukatar da ake da ita ta karfafa dangantaka a mataki na kasa da kasa ,

Daga kare Araqchi yayi tir da barazanar Amurka da kuma ayyukan ruwa da take yi a yankin karebiya, kuma ya bayyana su a matsayin keta dokokin kasa da kasa , da  yarjejeniyar majalisar dinkin duniya kana ya bayyana goyon bayansa ga kasar Venuzuwela, kuma yayi kira ga kasashen duniya da su nuna adawa da duk wani mataki na hade kai kan wata kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted