Ministan tsaron kasar Pakistan Sajjad Raufi ya gana da jakadan Iran a birnin Islam Abad Amir Ridha Mukaddam kuma sun tattauna kan yadda kasashen za su kara fadada dangantakar su ta fuskar tsaro da kuma yin aiki tare wajen yaki da ta’addanci da kuma kare iyakokin kasashen biyu dake makwabtaka da juna.
Wannan tattaunawar ta zo ne a sailin ziyarar da shugaban kasar Iran Ibrahim Ra’isi ya kai a kasar, kuma dukkan bangarorin sun jaddada muhimmanci yin amfani da kwarewar da suke da shi wajen yin aiki tare a bangaren tsaro da zimmar ganin an tabbatar da zaman lafiya da tsaro a iyakokin kasashen biyu da suka yi tarayya.
Ana sa bangaren ministan tsaron kasar Pakistan Khoja mohammad Asif a lokacin ganawar ya bayyana jin dadinsa na kara kyautatuwar alaka tsakanin kasashen guda biyu mai dadden tarihi, kuma ya bukaci a gaggauta kafa kwamitin hadin guiwa da zai sa ido sosai kan iyakokin kasashen biyu makwabtan juna.