Search
Close this search box.

Iran Tana Halattar Babban Taro Kan Ayyukan Fasaha A Kasar Italiya

JMI tana halattar taron baje kolin fasaha mafi girma a duniya a karo na 9 wanda ake gudanarwa a halin yanzu a kasar Italiya. Kamfanin

JMI tana halattar taron baje kolin fasaha mafi girma a duniya a karo na 9 wanda ake gudanarwa a halin yanzu a kasar Italiya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa an bude dakin ayyukan fasaha na kasar Iran a taron baje kolin fasahar ne tare da halattar jakadan kasar Iran a Italiya, Muhammad Reza Saburi da kuma jami’I mai kula da harkokin fasaha a ofishin jakadancin kasar Iran Muhammad Taqii Amini.

Ana gudanar da taron ayyukan fasaha na duniya ne a ko wani shekaru bibu, kuma wannan shi ne karo na 60 kenan. 

Saburi, a jawabin da ya gabatar a lokacin bude dakin JMI a taron ya bayyana cewa  an sanyawa taron na bana ‘Mutane gabban ko wannensu ne” . Ya kuma kara da cibiyar ayyukan fasa na Iran dake Tehran ta taimaka wajen kawo kayakin fasahar da ake bukara zuwa kasar Italiya don baje kolin ayyukan fasaha na JMI.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments