Mutanen a kasashen duniya da dama suna ci gaba da zanga zangar goyon bayan al-ummar Falasdinu da kuma yin allawadai da HKI.
Kamfanin dillancin labaran IRIB.NEWS na kasar Iran ya bayyana cewa mutanen musamman daliban jami’o’ii a a birnin Wanariya a kasar Italia, Tokyo na kasar Japan, Al-Jadida na kasar Morokko, Rotadam na kasar Holan, da kuma unguwar manhatan na birnin NewYork na kasar Amurka duk sun fito don nuna goyon bayansu ga Al-ummar Gaza, da kuma yin tir da HKI.
Sauran kasashen sun hada da Jamus da kanada, banda haka, mutane sun yi allawadai da siyasar shuwagabannin kungiyar G7 masu karfin tattalin arziki a duniya.
Tun ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ne HKI ta farwa falasdinawa a gaza da manufar kwato yahudawan da kungiyar Hamas ta kama a matsugunansu da suke gawaye da yankin, da kuma shafe kungiyar Hamas daga doron kasar. A halin yanzu shekaru 75 kenan da mamayar kasar Falasdinu da kuma korar wasu daga cikin falasdinawa daga kasarsu, wanda HKI tare da taimakon kasashen yamma take yi, take kuma ci gaba da yi.