Kasashen Duniya Na Yin Kira Da Tsagaita Wuta Na Wucibn Gadi A Yakin Lebanon Da Isra’ila

Amurka da Tarayyar Turai na  jagorantar yunkurin diflomasiyya a birnin New York, don kaucewa barkewar mummunan yaki tsakanin  Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda suke

Amurka da Tarayyar Turai na  jagorantar yunkurin diflomasiyya a birnin New York, don kaucewa barkewar mummunan yaki tsakanin  Lebanon da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda suke yin kira da a cimma matsaya ta wucin gadi, da kuma ci gaba da kokarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza.

Wata sanarwar hadin gwiwa da Amurka da Tarayyar Turai suka da kuma  kasashen Larabawa suka fitar, sun kira da a tsagaita bude wuta na wucin gadi a Lebanon.

Wani jami’in Amurka ya fada a cikin wani taron manema labarai cewa “nassin shawarwarin zai kunshi matsayar  bangarorin Isra’ila da na Lebanon kafin a buga shi.”

A nasa bangaren, wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya yi nuni da cewa “shawarar da ke magana kan tsagaita wuta ta kwanaki 21 ta takaita ne ga bangaren Lebanon kawai.”

Wata sanarwar hadin gwiwa da shugaban Amurka Joe Biden da na Faransa Emmanuel Macron suka fitar ta tabbatar da cewa , lokaci ya yi da za a cimma matsaya kan iyakar Lebanon da Isra’ila a cewarsa, wanda hakan zai baiwa fararen hula na bangaririn biyu damar komawa gidajensu.

Sanarwar ta sami goyon bayan Amurka, Australia, Kanada, Tarayyar Turai, Faransa, Jamus, Italiya, Japan, Saudi Arabia, Emirates da Qatar, inda kuma suke yin kira ga Lebanon da Isra’ila da su amince da hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments