Kasar Sin za ta karbi bakuncin shawarwarin sulhu na Fatah da Hamas

Tawagogin da suka fito daga manyan kungiyoyin Falasdinawa biyu, wato kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da kuma jam’iyyar siyasa ta Fatah, za su gudanar da shawarwarin

Tawagogin da suka fito daga manyan kungiyoyin Falasdinawa biyu, wato kungiyar gwagwarmaya ta Hamas da kuma jam’iyyar siyasa ta Fatah, za su gudanar da shawarwarin sulhu a birnin Beijing nan gaba kadan.

Wakilan kungiyoyin za su gana da jami’an kasar Sin a ranar 20 ga watan Yuli da 21 ga watan Yuli, in ji mataimakin babban sakataren kwamitin kolin Fatah, Sabri Saidam a ranar Litinin.

Tawagar Hamas za ta kasance karkashin jagorancin shugaban ofishin siyasa na kungiyar Ismail Haniyeh, yayin da tawagar Fatah za ta kasance karkashin mataimakin shugaban kungiyar Mahmoud al-Aloul.

Fatah da Hamas dai sun kasance cikin rashin jituwa tun bayan da suka samu gagarumin rinjaye a zaben Falasdinawa a shekara ta 2006. Hamas ce ke mulkin zirin Gaza, yayin da Fatah ta kafa ofisoshi a yammacin gabar kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Bangarorin sun amince a watan Afrilun 2014 don kawo karshen korafe-korafensu da sasantawa. Matakin ya jawo fushin jami’an Isra’ila, kuma gwamnatin Tel Aviv ta mayar da martani ta hanyar dakatar da tattaunawar da ake kira “zaman lafiya” da hukumar Falasdinu, wadda Fatah ke jagoranta.

Bayan yarjejeniyar, bangarorin biyu sun kafa gwamnatin hadin kan kasa, wacce Fatah ta rusa shi a cikin watan Yunin 2015, tana mai cewa “kwamitin yana da rauni,” kuma Hamas ba za ta “bar ta ta yi aiki a Gaza ba.”

Saidam ya ce, Manufar taron na Beijing , “shi ne kawo karshen yanayin rarrabuwar kawuna tare da kudurin cimma yarjejeniyoyin da suka gabata da kuma cimma matsaya kan dangantaka tsakanin kungiyoyin Falasdinu a mataki na gaba.”

Wani mamban zartarwa na Fatah ya kuma ce za a iya gudanar da taron hadin gwiwa na Fatah da Hamas a birnin Beijing kafin a fara aiwatar da ajandar hukumarwa Falastinawa.

China ta karbi bakuncin Fatah da Hamas a watan Afrilu, amma an dage taron da aka shirya yi a watan Yuni.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments