Wakilan gwamnatin Kamaru sun gana da jami’an matatar man fetur din Dangote, da zummar kulla yarjejeniyar kasuwanci, bisa la’akari da yadda kasar ke fuskantar koma baya a bangaren samar da wadataccen man fetur, lamarin da ya haifar wa da kasar bashin CFA biliyan 479 a koƙarinta na neman cike gibin da ake samu.
Babban jami’in matatar man Kamaru, El Hadj Bako Harouna ne ya jagoranci tawagar jami’an kasar da suka gana da takwarorinsu na matatar Dangote a birnin Legas, inda suka shafe kwanki 3 suna tattaunawar da ta mayar da hankali kan yadda matatar man Kamarun ta Sonara za ta farfado gami da neman tallafin kwararru daga matatar Dangote.
A cewar wakilan na Sonara, babban kudirinsu shi ne kafa tubalin da zai tallafawa kasar su wajen samar da wadataccen man fetur ga ‘yan Kamaru, domin zama masu dogaro da kai a bangaren samar da makamashi.
A cikin Sabon tsarin, anasa ran ya fara aiki tsakanin wannan shekara zuwa 2027 dan samun damar farfado da Matatar na Sonara da gobara ta sa aka rufeshi, a 2019.