Kasar Iran Ta Nuna Rashin Amincewa Da Ikrarin Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da wasikar nuna rashin amincewa ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan zargin karya da kungiyar hadin kan

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta aike da wasikar nuna rashin amincewa ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan zargin karya da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi kanta

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran kuma wakilinta na din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’id Irawani ya aike da wasikar nuna rashin amincewa ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan zargin karya da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ke yi kan kasarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarto daga cibiyar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin New York na kasar Amurka cewa: Amir Sa’id Irawani bayan kokawa kan zargi maras tushe da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ta yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya yi kuma kakkausar suka da kuma yin watsi da zargin rashin adalci maras tushe da ake yi wa ‘yancin kan Iran da kasarta, wanda ya zo a cikin sakin layi na 11 na sanarwar kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, tare da daukar wannan mataki a matsayin tsoma baki aharkokin cikin gidan Iran kuma rashin adalci kan al’amuran da suka shafi kasar Iran.

Wannan wasikar ta kara da cewa: Wannan matakin ba wai kawai ya saba wa ruhin kyakkyawar makwabtaka ba ne, a’a, yana kuma taka rawa wajen keta ka’idojin dokokin kasa da kasa da kuma kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, musamman ma ka’idojin daidaito da rashin tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasashe. Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake jaddada ikonta a kan tsibiran Abu Musa, da Tunbu Babba, da kuma Tunbu Karami  da suke gabar tekun Farisa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments