Kasar Iran Ta Ce Ba Ta Wani Shirin Boye A Hukumar Makamashin Nukiliyarta

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba ta da shirin nukiliya na sirri Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami,

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba ta da shirin nukiliya na sirri

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Eslami, ya tabbatar da cewa; Iran ba ta da shirin nukiliya na sirri, inda duk shirinta yake gudana karkashin sa idon Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta duniya IAEA.

Islami ya kara da cewa: Makiya masu adawa da ci gaba Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun yi da’awa a cikin fayil ɗin nukiliyar Iran cewa kasar tana da wani Shirin sirri da ba ta bayyana ba kan shirinta na nukiliya, kuma da waɗannan dabaru da makircin siyasa sun shafe shekaru 20 suna daukan matakan matsin lamba kan hukumar makamashin nukiliyar Iran.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta rattaba hannu kan shirin aiwatar da aikin hadin gwiwa da Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya IAEA, kuma an cimma yarjejeniyoyin da ita, amma bayan wani lokaci, Amurka ta yanke shawarar ficewa daga wannan yarjejeniya kuma shugabata na wancan lokaci Donald Trump ya fice daga wannan yarjejeniya a wancan lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments