Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta bayyana cewa: Amurka tana kalubalantar cibiyoyin kasashen Duniya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Dabi’ar Amurka ta aiwatar da dokokin cikin gida ta ketara kan iyakokinta, inda a yanzu take tunkarar cibiyoyin kasa da kasa.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya rubuta a shafin dandalin “X” dangane da sakamakon takunkumin da Amurka ta kakabawa cibiyoyin kasa da kasa misalin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya a matsayin tarayya a tafka laifuka da gwamnatin mamayar Isra’ila, yana mai jaddada cewa: Amurka ta ketara haddinta na aiwatar da dokokin a cikin gidan kasarta, ta ketara kan iyakokinta yanzu kan cibiyoyin kasa da kasa.
Baqa’i ya kara da cewa: Kakaba takunkumi kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa domin gudanar da bincike kan munanan laifukan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, wani abu ne da ba a taba ganin irinsa ba a tsawon tarihin Amurka na hada baki da wani gungun ‘yan mamaya masu nuna wariyar al’umma wadanda suke aikata muggan laifuka iri-iri ciki har da aiwatar da kisan kare dangi kan al’ummar Falastinu.