Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Mayakan kungiyoyin ‘yan ta’addan kasar Siriya sun yi kuskure a lissafinsu
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Araqchi ya bayyana a lokacin da ya isa birnin Ankara na kasar Turkiyya cewa: ‘Yan ta’addan Siriya sun tafka kura-kurai a lissafinsu, kuma sojojin gwamnatin kasar na iya kalubalantarsu.
Araqchi ya shaidawa ‘yan jaridu da sanyin safiyar yau Litinin da ya isa birnin Ankara fadar mulkin kasar Turkiyya game da ziyarar da ya kai Damascus fadar mulkin kasar Siriya da kuma ganawarsa da shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad cewa: Ganawarsa da shugaba Bashar al-al-Assad ta yi kyau sosai kuma sun tattauna batutuwa masu muhimmanci da neman hanyar warware matsalar da ta kunno kai a Siriya.
Araqchi ya kara da cewa: Iran da kungiyoyin gwagwarmaya suna goyon bayan Siriya wajen tunkarar ‘yan ta’adda, kuma suna da alaka da kyakkyawar alaka da Turkiyya wajen ganin an wanzar da zaman lafiya a Siriya, sannan suna fatan samun fahimtar juna kan zaman lafiya a dukkanin yankin.
Ministan harkokin wajen Iran ya kuma jaddada cewa: Suna ci gaba da musayar ra’ayi sosai kan abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya da kuma dukkan yankin.