Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke da goyon bayan al’ummar Siriya
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i ya tabbatar a yau Litinin, a taron manema labarai na mako-mako cewa: Iran tana goyon bayan duk wata gwamnati da ke samun goyon bayan al’ummar Siriya.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya gudanar ya amsa tambayoyin ‘yan jaridu dangane da batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa da kuma huldar diflomasiyyar Iran.
Baqa’i ya tabo batun ziyarar da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya kai zuwa kasar Qatar, inda ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne bisa tsarin alakar diflomasiyya ta al’ada tsakanin kasashen biyu. Ya kara da cewa: Iran tana da kyakkyawar alaka da Qatar, kuma suna ci gaba da tuntubar juna kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaban yankin.