Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”.
A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Banjul a ranar 27 ga watan Febrairu a karkashin wata yarjejeniya da aka cimmawa a tsakanin kasashen yankin domin lalubo hanyar warware takaddamar siyasar da kasar Kamaru take fama da ita.
Tun bayan da Chiroma ya fice daga kasar ta Kamaru, ya nufi kasar Najeriya, mahukunta a kasar tasa suke kiran da a kama shi.
Sai dai maimakon haka, gwamnatin kasar ta Najeriya ta cimma matsaya da mahukuntan kasar Gambia akan a bai wa Chiroma din mafaka a can bisa sharadin cewa ba zai rika gudanar da wasu ayyuka na siyasa ba.
Tun bayan zaben shugaban kasa ne dai kasar ta Kamaru ta fada cikin dambaruwar siyasa wacce ta kai ga dakatar da harkokin yau da kullum a cikin manyan birane. Dan takarar jam’iyar Adawa, Isa Chiroma ya riya cewa shi ne ya lashe zaben, tare da zargin hukumar zabe da yin magudi saboda bai wa Paul Biya damar ci gaba da zama akan kujerar mulki.