Ministan harkokin wajen kasar ta Denmaka ya ce; Mazauna yankin Greenland za su iya zama kasa mai ‘yanci idan su su ka bukaci hakan, amma dai ba za ta taba zama jaha a karkashin Amurka ba.
Wannan martanin dai ya zo ne bayan da zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa; Kasarsa za ta iya amfani da karfin soja domin shimfida ikonta akan yankin Greenland domin kare manufofinta na tsaron kasa.
Bayan wannan furucin na Trump ne dai shugaban yankin na Greenland ya tttauna da sarkin Denmark a birnin Copenhagen akan wannna barazana.
A ranar Talata da Donald Trump ya yi wancan furuci ya kuma aike da dansa zuwa wannan yankin na Greenland inda ya tattauna da shugabanninsa.
Yankin Greenland dai shi ne tsibiri mafi girma a duniya kuma ya dauki shekaru 600 a karkashin ikon masarautar Denmark. Yankin mai mutane 57,000 yana da kwarya-kwaryar cin gashin kai.
Ministan harkokin wajen Denmark Lars Lokke ya ce, yana da masaniya akan cewa; yankin Greenland yana da nashi shirin da tanadin da idan su ka kamala zai iya zama kasa mai ‘yanci,amma ba za su taba zama a karkashin Amurka ba.
.