Rahotanni sun bayyana cewa Wang Yi ministan harkokin wajen kasar china a sailin taron kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a birnin NewYork ya fadi cewa kasarsa tana goyon bayan sanya yankin falasdinawa a matsayin cikakkiyar mamba a kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a amatsayin kasa mai cin gashin kanta.
Yace hare haren da Isra’ila ta kaddamar a yankin gaza ya haifar da mummunan yanayi ga bil adama kuma kasar china tana kira da a gaggauta dakatar da bude wuta ba tare da wani sharadi ba, kuma ta bukaci a dauki wasu matakai da zasu taimaka wajen ganin an takaita yi yuwar barkewar rikici a yankin
Idan ana iya tunawa a baya bayan nan ne hukumar falasdinu ta bukaci kwamitin tsaro ta majalisar dinkin duniya ya sake duba bukatarta ta neman kasancewa mamba a majalisar, a karon farko a shekara ta 2011 gwamnatin falasdinu ta gabatar da bukatar ta ta kasancewa mamba mai cin gashin kai a majalisar dinkin duniya