Kanada Ta Tsare Tsohon Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Mai Bincike Kan Laifukan Yakin Israila.  

Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar

Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar a kasar kanada inda aka tsare shi tare da yi masa tambayoyi  a wata tafiya da yayi don halartar taron dake da alaka da yankin Gaza.

Falka dan shekara 92 da haihuwa, hukumar kula da hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta nada shi a shekara ta 2008 na tsawon shekaru 6 a matsayin dan rahoton musamman don gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka a yankin falasdinu.

Falk ya bayyana cewa dalilin yin tambayoyi na tsawon lokaci  ga manyan masana da ba sa yin wata barazanar tsaro a filin saukar jiragen zama na Toranto  wani makirci ne na ladabtar da wadanda suka sadaukar da kansu fadin gaskiya kan abin da ke faruwa ga alummar falasdinu musamman ma yankin gaza ga duniya.

Sojojin isra’ila sun kashe falasdinawa akalla 69187 a yankin Gaza mafi yawanci mata ne da yara kanan tare da jikkata 170708 tun watan oktoban shekara ta 2023

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted