Kafafen watsa labarun HKI sun nakalto cewa kamfanin jirgin saman kasar Oman, wato “Oman Air” ya cire sunan Isra’ila daga cikin taswirarsa yam aye gurbinta da Falasdinu, domin nunawa domin abinda yake faruwa.
Tashar talbijin din “almayadin’ ce ta nakalto labarin daga kafafen watsa labarun HKI akan matakin na kasar Oman.
Ana ganin matakin na Oman a matsayin mayar da martani akan kisan kiyashin da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, musamman a Gaza.
A baya ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu, domin kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, da kuma buke kafar da za a shigar da kayan abinci da bukatun yau da kullum cikin yankin na Gaza.
HKI tana fuskantar matsin lamba da kuma zama saniyar ware daga kasashen duniya saboda kisan kare dangin da take yi wa al’ummar Falasdinu, musamman a Gaza.
Ya zuwa yanzu wadanda su ka yi shahada sun haura 67,000 yayin da wasu dubun dubata su ka jikkata.
A yau 7 ga watan Oktoba ne dai ake cika shekaru biyu da shelanta yakin da HKI ta yi akan al’ummar Falasdinu.