Kamfanin Hakar Uranium Na Faransa Ya Tafka Asara, Bayan Da Sojoji Suka Kore Shi A Nijar

Kamfanin samar da makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya sanar da tafka asara ta Yuro miliyan 133 sakamakon matsalolin da yake fuskanta wajen gudanar da

Kamfanin samar da makamashin nukiliya na Faransa Orano, ya sanar da tafka asara ta Yuro miliyan 133 sakamakon matsalolin da yake fuskanta wajen gudanar da ayyukan hakar ma’adinai tun bayan zuwan sabbin mahukuntan mulkin soji a Jamhuriyar Nijar.

Kamfanin ya ce ya tafka wannan asara ce a cikin watanni shida saboda matsalolin da yake fuskanta a kasar ta Nijar, in ji darektan kudi na kungiyar David Claverie.

A alkalumman da kamfanin ya fitar ranar Juma’a, ya ce sabanin watannin uku farko na shekarar 2023 data gabata, inda ya samu ribar Yuro miliyan 117.

Wannan na da nasaba ne da kwace masa lasisin aiki a mahakar uranium ta Imouraren da humomin mulkin sojin Nijar sukayi a wata Yuni da ya gabata, sai kuma wasu kadarorin reshensa na Somaïr dake cikin tsaka mai wuya.

Danganta tsakanin Nijar da kuma Faransa wacce ta yi mata mulkin mallaka ta yi tsami ne tun bayan da sojoji suka kifar da mulkin tsohon shugaban kasar Mohamed Bazoum, shekara guda da ta gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments