Babban attajirin nahiyar Afirka Alhaji Aliko Dangote na Shirin zuba hannun jari na dalar Amurka biliyan 16 a Babbar matatar man fetur a kasar Kenya wacce ya bayyana da cewa: Wani sabon shafi ne a fagen kafa masana’antu a Afirka.”
Kafa matatar dai zai dauki watanni 30 zuwa 40 a kammala ta,ta fara fuskantar kalubalanta daga mutanen yankin da za a yi ginin akan hakkin mallakar filaye.
Sabuwar matatar idan an kammala ta za ta rika tace man fetur da zai kai ganga 700,000 a kowace rana.
A can kasarsa ta haihuwa Aliko Dangote ya kafa matatar man fetur da ita ce mafi girma a nahiyar Afirka.
Aliko Dangote ya ce; Aikin kafa matatar tana nufin kasashen Afirka za su hada kai wuri daya domin gina nahiyar Afirka. Abinda muke yi a wannan lokacin shi ne share fagen bude sabon shafi na gina masana’antu a cikin nahiyar Afirka.”
Sai dai masu kare muhalli sun fara daga murya suna yin koke akan tasirin gina matatar a yankin Lamu, wanda yana cikin wuraren yawon bude ido,kuma mazaunin masu Magana da harshen Swahili mafi dadewa tun a karni na 12.