Kamala Harin Na Kara Samun Goyan Baya Daga ‘Yan Democrats

Manyan yan jam’iyyar Democrats a Amurka na ci gaba da nuna goyon bayansu ga mataimakiyar shugaban kasar a matsayin ‘yar takara bayan janyewar shugaba Biden.

Manyan yan jam’iyyar Democrats a Amurka na ci gaba da nuna goyon bayansu ga mataimakiyar shugaban kasar a matsayin ‘yar takara bayan janyewar shugaba Biden.

Gwamnan jihar Carlifonia Gavin Newsom daya daga cikin wadanda ake ganin za su fito su kalubalance ta ya sanar da mara mata baya.

Tuni gwamnoni uku, da sanatoci takwas da gwamman ‘yan majalisar wakilai suka sanar da goya mata baya.

Haka ma tsohon shugaban kasar Bill Clinton da matarsa ​​Hillary Clinton da wasu mashahuran ‘yan fim da mawaka na Hollywood sun ce suna tare da ita.

A jiya ne shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da janyewa daga neman sake tsayawa takarar shugabancin kasar bayan wasu ‘yan jam’iyyarsa ta Democrat sun matsa masa lamba don ya hakuri da takarar sakamakon rashin cikakkiyar lafiyar kwakwalwa.

A wani sako da Biden ya wallafa a shafin X, ya ce zai ci gaba da ayyukansa na shugaban Amurka kuma babban kwamandan tsaron kasar har karshen wa’adin mulkinsa na farko a watan Janairun 2025 kuma zai yi wa ‘yan kasar jawabi a wannan makon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments