Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Ya Jaddada Gagarumin Tsaron Kasa Da Gwagwarmaya Ta Baiwa Lebanon

Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon

Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon ya bayyana cewa; Gwagwarmaya ta tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila rashin girke sojojinta a kan iyakar da ke tsakanin Isra’ila da Lebanon

Kakakin Majalisar Dokokin Lebanon Nabih Berri ya tabbatar da cewa: “Gwagwarmaya ta yi cikakken biyayya ga sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma sojojin Lebanon sun tura sojoji da jami’ai sama da 9,000 a yankin da ke kudancin Kogin Litani.” Ya ƙara da cewa “sojojin suna da ikon tura sojoji a kan iyakokin da ƙasashen duniya suka amince da su tsakanin Labanon da Isra’ila, amma abin da ke kawo cikas ga wannan shi ne ci gaba da mamaye yanki mai girma na kudancin Lebanon da sojojin mamayar Isra’ila suka yi, kamar yadda Rundunar UNIFIL da rahotanninta na lokaci-lokaci suka tabbatar da hakan.”

Jawabin Kakakin Majalisar Dokokin Berri ya zo ne a ranar Talata yayin wani taro a hedikwatar Shugaban Ƙasa ta Biyu da ke Ain al-Tineh tare da tawagar kungiyar gidajen Rediyo da Talabijin ta Musulunci. Ya ce, “Amma tambayar da dole ne a yi ita ce: yaushe, a ina, kuma ta yaya Isra’ila ta bi ko da sashe ɗaya na yarjejeniyar tsagaita wuta?” Ya bayyana mamaki da “matsayin wasu a cikin Lebanon game da yadda suke nuna adawa ga ‘yan gwagwarmaya,” yana mai cewa “waɗannan mutane suna ƙin ambaton kalmar ‘gwagwarmaya’ a cikin kowace tattaunawa ta siyasa ko ta kafofin watsa labarai.” Yana mai tambayar cewa: “Shin akwai wata ƙasa a duniya da ta musanta babi mafi tsarki na tarihinta?”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments