Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya jaddada cewa: “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a shawarwari,” yana mai bayanin cewa: “Tun bayan barkewar yaki da Iran, kasar Iran ta daina yin mu’amala da Amurkawa, amma tana ci gaba da hulda da Turawa ko da a lokacin da ake tsaka da yakin.”
A wata hira da jaridar Süddeutsche Zeitung ta Jamus dangane da shawarar da Turai ta gabatar na tsawaita wa’adin aiki da hanyar da za a bi wajen ganin an dawo da takunkumin majalisar dinkin duniya kan Iran, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Iran ta yi imanin cewa, ko wanne lokaci, ko tsawaitawa takunkumi, ko kuma ci gaba da aiki da shi, ba ya dogara ne akan dalilai na shari’a, da ma’ana, ko kuma kyawawan dabi’u ba.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: “Babu wata hujjar cewa shirin makamashin nukiliyar Iran ya ci gaba da kasancewa karkashin kulawar kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, musamman ganin cewa ba a yin shawarwari cikin yanayi na yau da kullum.”
Baqa’i ya yi nuni da cewa: “An kai wa Iran hari ne a tsakiyar tattaunawar, don haka tana da ‘yancin neman sauran bangarorin su tabbatar da amincinsu.” Ya kara da cewa, “Turawa za su iya taka muhimmiyar rawa a cikin wannan tsari, tun bayan barkewar wannan yakin, Iran ta daina hulda da Amurkawa, amma tana hulda da Turawa ko da a lokacin yakin.”