Search
Close this search box.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Masu Goyon Bayan Zalunci, Azzalumai Ne

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Masu goyon bayan yahudawan sahayoniyya suna da hannu wajen ci gaba da aikata muggan laifuka a

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Masu goyon bayan yahudawan sahayoniyya suna da hannu wajen ci gaba da aikata muggan laifuka a Gaza

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Alhakin Amurka da sauran bangarorin da suke goyon bayan ‘yan sahayoniyya tare da tallafa musu da muggan makamai wajen ci gaba da aikata munanan laifuffuka, bai kasa na gwamnatin yahudawan sahayoniyya da suke aiwatar da laifuffukan kai tsaye ba.

Nasir Kan’ani ya bayyana a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa: Ba za a iya misalta azaba da radadin da Falasdinawan suke ciki da kuma mazauna Zirin Gaza ba. Ya kara da cewa: Alhakin Amurka da sauran bangarorin da suke goyon bayan ‘yan sahayoniyya a ci gaba da wadannan munanan laifuka, bai kasa alhakin masu aiwatar da laifukan kai tsaye ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments