Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Masu Goyon Bayan Isra’ila Suna Da Hannu A Laifukanta

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, kuma magoya bayanta suna da hannu a ciki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, kuma magoya bayanta suna da hannu a ciki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa:                               Rahoton kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa, laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Gaza sun kai na “kisan kare dangi”, inda ya yi kira ga masu kare gwamnatin ta Isra’ila da su daina shiga da hada baki wajen aikata wadannan laifuka kan al’ummar Falastinu.

Baqa’i ya bayyana cewa: Kwamitin bincike mai zaman kansa na kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan da ake aikatawa a Falasdinu da aka mamaye karkashin jagorancin fitacciyar marubuciya Navi Pillay, ba ta da wata shakka game da irin laifukan da kuma irin zaluncin da ake yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa, hukumar ta tabbatar a cikin wani bincike na shari’a mai shafuka 72 na gaskiya da alkaluma, cewa haramtacciyar kasar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments