Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta sanar da cewa: Kasashen yammacin duniya sun rasa mutuncinsu da daukakarsu sakamakon yakin Gaza
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: Kasashen yammacin duniya sun rasa mutuncinsu da martabarsu sakamakon yakin da ake yi a Zirin Gaza, kuma sun fuskanci rugujewar dabi’a da koma bayan wayewa.
Nasir Kan’ani ya rubuta a cikin wani sako a shafinsa na sada zumunta cewa: A cikin kundin tarihin Amurka da Turai, mutane da ƙungiyoyin da ke kare ƙasarsu daga sojojin mamaya kuma suna yaƙi don kare gidajensu, iyalansu, da mutuncinsu na ɗan adamtaka daga wasu gungun sojoji masu dauke da makamai da suke kashe yara da mata, kuma ’yan ta’adda ne, wasu jama’a ne suke goyon bayan wadannan mutane da ake zalunta, shin wadanda suke goyon bayan ayyukan ta’addanci!
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da take aiwatar da kisan gilla tare da kashe mutane sama da 40,000 a cikin watanni 10 kuma kusan 10,000 daga cikinsu yara, amma ba a daukansu ‘yan ta’adda, iyaka ma sun cancanci karfafa musu karfin gwiwa da kowane nau’in siyasa, tsaro, tallafin soja da makamai!
Kan’ani ya jaddada cewa: wadannan munanan ayyukan kasashen Yamma sun sanya sun rasa mutuncinsu da martabarsu a yakin Gaza tare da fama da fuskantar matsalar rugujewar kyawawan dabi’u da tabarbarewar al’adu.