Tashar talabijin na yahudawan sahayoniyya ta bayyana adadin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suka halaka a cikin makonnin da suka gabata
Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun bayyana irin hasarar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi na sojojinta a Zirin Gaza, sakamakon turjiya da tsayin dakan ‘yan gwagwarmayar Falastinawa musamman a yankuna daban-daban da sojojin haramtacciyar kasar ta Isra’ila suka kutse cikinsu a zirin na Gaza.
Tashar talabijin ta 13 haramtacciyar kasar Isra’ila a jiya Talata ta ce: An kashe sojojin yahudawan shayoniyya 7 a fadace-fadacen da aka gwabza a zirin Gaza a cikin kwanaki hudun da suka gabata, ciki har da sojoji 4 da suka halaka sakamakon fashewar wasu bama-bamai.
Kamar yadda tashar talabijin ta Kan ta 11 ta watsa rahoton cewa: Adadin sojojin da aka kashe a zirin Gaza a cikin makonnin da suka gabata ya zarce adadin sojoji maza da mata da aka kashe a lokacin harin Ambaliyar Al-Aqsa a ranar 7 ga watan Oktoban bara, da kuma a kwanakin da suka gabaci a kai hari ta kasa kan Gaza.