Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar.
Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi.
Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya.
Yansan da a birnin Stokhom sun tabbatar da c ewa sun ji karar bindiga a kudancin birnin a daren laraba, amma a lokacinda suka isa wurin sai suka sami wani mutum da harbin birnin. Amma bai dade bay a mutu.
Mai sharia Goran Lundahl na birnin ya tabbatar da cewa gawar ta Sewan ne amma har yanzun basu da masaniya kan yadda aka kashe shi.