Shugaban majalisar dattijan kasar Jordan Faisal Al-Fayez ya jaddada a ranar Juma’a cewa: Ana daukar kasarsa a matsayin ginshikin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai cewa; Duk wani hargitsin da zai iya faruwa a kasar, zai shafi kasashen yankin baki daya, yana mai jaddada cewa: Kasashen yamma, musamman Amurka, suna da cikakkiyar masaniya game da wannan lamari.
Al-Fayez ya bayyana cewa, a cikin hirarsa da tashar talabijin ta masarautar Jordan kan manyan kalubale da kasarsa ta fuskanta a baya, amma ta yi galaba a kansu da karfi da kuma tsayin daka, tare da dogaro da muhimman abubuwa, wadanda mafi muhimmancinsu su ne tsaro da zaman lafiyarta, yana mai cewa, diflomasiyyar kasar Jordan tana da babban karfin wajen samar da daidaito, kamar yadda sarkin Jordan Abdallah na biyu ya yi nasara a fagen gudanar da kyakkyawar alakar kasarsa da kasashen yanki da na kasa da kasa wajen nisanta hatsarori da dama.