Jiragen Yakin HKI Sun Sun Yi Luguden Wuta A Kan Wasu Karin Sansanonin Sojojin Kasar Siriya

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta kan karin sansanonin sojojin kasar Siriya, a daren jumma’an da ta gabata. Kuma wuraren sun hada da birnin

Jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta kan karin sansanonin sojojin kasar Siriya, a daren jumma’an da ta gabata. Kuma wuraren sun hada da birnin Damascus babban birnin kasar, Hama, Lantakia da kuma Suwayda.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan sansanonin sojojin kasar Siriya fiye da 20 a jiya da dare.

Labarin ya kara da cewa jiragen HKI sun yi luguden wuta a kan runduna ta 4 inda aka girka na’urorin Rada a wajen birnin Damascus babban birnin kasar.

Haka ma, sun kai hare-hare kan na’uran Rada a kan tsaunukan Qasyon, a wajen birnin Damascus, babban birnin kasar. Hare-hare na Qasyon sun girgiza birnin na Damascus saboda karfinsu.

Har’ila yau jiragen yakin yahuadwan sun kai hare–hare kan tashar jiragen sama ta Khalkhala a lardin Suwayda wanda yake kan iyaka da kasar Jordan, tare da amfani da makamai masu linzami.

Banda haka masu sanya ido kan al-amuran yaki a kasar Siriya, suna cewa, jiragen yakin HKI sun yi luguden wuta kan wurare 6 a  Dimashq da kuma Al-Suwayda.

Banda haka sun kai hare–hare kan runbun ajiyar makamai, da kamfanonin kera makamaoi, da cibiyar binciken ayyukan soje na kasar Siriya, wanda ake kira Misyaf a yammacin garin Hama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments