Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare-Hare Kan Birnin Hudaida Na Kasar Yemen A Safiyar Yau Talata

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan birnin Hudaidah na bakin ruwa a kasar Yemen a safiyar yau Talata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar

Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan birnin Hudaidah na bakin ruwa a kasar Yemen a safiyar yau Talata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto tashoshin talabijin ta Almasirahtv ta kasar Yemen, da kuma Aljazeerah ta kasar Qatar  suna bada wannan labarin.

Sun kuma kara da cewa tun fara yaki a Gaza a shekara ta 2023 sojojin kasar Yemen suka hana jiragen kasuwanci na HKI wucewa ta babul Mandab na kasar Yemen wanda ya jawowa HKI asarori masu yawa, ya kuma gurgurta ayyukan tashoshin jiragen Ruwa na ummu Rashrash ko Ilat da kuma Haifa.

Sannan suna kaiwa hki hare-hare ne da makamai masu linzami kan tashar jiragen sama na Bengerion da kuma wuraren soje na kasar tun lokacin

Yemen na yin haka ne don goyon bayan  ga al-ummar Falasdinawa wadanda sojojin HKI suke ci gaba da yi masu kisan kare dangi tun lokaci har zuwa yanzu. Falasdinawa kimani 54000 hki ta kace ya zuwa yanzu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments