Jiragen yakin kasashen Amurka da Burtania sun kai hare haren ta’addanci a kan lardin Taiz na kasar Yemen a safiyar yau Jumma’a.
Tashar talabijin ta Almsirah ta kasar Yemen ta bayyana cewa jiragen yakin Amurka da Burtaniya sun kai hare hare har guda 4 a lardin Taiz, wadanda suka hada da garuruwan Dhahra da kuma Mawiyah na lardin.
Shafin yanar gizo na Almasirah ya bayyana cewa kasashen biyu suna sun hana gwamnatin kasar Yemen aiwatar da matakan da ta dauka na hana jiragen ruwan HKI bin da tekun Red Sea da kuma Tekun India, don nuna goyon bayanta ga Falasdinawa a Gaza, wadanda sojojin HKI suke yi wa kissan kiyashi.
Gwamnatin kasar Yemen ta bayyana goyon bayanta a fili ga Falasdinawa tun farkon yakin Tufanul aksa wanda kungiyar Hamas ta fara a ranar 7 ga watan octoban shekarar da ta gabata.