A safiyar yau ne jiragen yakin HKI suka kai hare-hare kan tashar Jiragen sama na birnin San’a na kasar Yemen inda ake ganin hakan kara ruruta wutan yaki a yankin ne.
Klamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a dai-dai lokacinda jiragen yakin Amurka suka dauki kimani watannin biyu suka kai hare hare kan kasar Yemen a yau jiragen yakin HKI sun kai wasu sabbin harehare a kan birnin san’a baban birnin kasar.
A cikin makon nan ne kungiyar Ansarulla.. ta kai hare hare da makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na bengerio tashar jiragen sama mafi girma, a kasar wanda ta dakatar da tashin jiragen sama na kwanaki sannan wasu dan kadan suka fara tashi tsakanin jiya da yau.
Kubgiyar Huthi ta ce zata maida martani mafi tsanani a kan HKI don tallafawa mutane gaza wadanda hki take gashewa da ta sama da makamaita kasa kuma da yunwa.
Kafafen yada labarai na HKI sun bayyana cewa jiragen yakin kasar sun kai hare hare har 15 a kan tashae jirasgen sama na san’aa kuma sun lalata ta gaba daya. Kungiyar an sarullah dai tace zata maida martani mai karfi a na gaba.