Jiragen Saman Yakin Sojojin Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Kasar Siriya

Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar Majiyoyin cikin gida na

Jiragen saman yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare kan yankunan birnin Damascus fadar mulkin Siriya da kuma yankin yammacin kasar

Majiyoyin cikin gida na kasar Siriya sun bayyana cewa: Jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin sojin Siriya bayan da suka yi shawagi a kan garuruwan Hama, Dar’a, Damascus, yankin kan iyakar Siriya da Lebanon da kuma gabar tekun Siriya.

Wadannan su ne fitattun abubuwan da suka faru a lokacin da jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai wa kasar Siriya hare—haren wuce gona da iri a yammacin ranar Juma’a.

Rahotonni sun kara da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare guda biyu kan birnin Al-Tall da ke cikin karkarar Damascus, sannan sun kai wasu hare-hare guda 6 a wajen babban birnin kasar, Damascus, yayin da jiragen yakin ‘yan mamayar suke ci gaba da shawagi a sararin samaniyar Dar’a, As-Suwaida, da Quneitra.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments