Jiragen sama marasa matuka ciki mallakin kungiyar Hizbullah sun kona sansanonin sojin yahudawan sahayoniyya na Sharaga da Nahariya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta kaddamar da wani hari ta hanyar jiragen sama marasa matuka ciki kan hedkwatar rundunar ta Golan da kuma bangaren hedkwatar Egoz 621 a barikin “Sharaga” da ke arewacin Akka da aka mamaye.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa: Wannan farmakin na zuwa ne a matsayin mayar da martani ga farmaki da kisan gilla da makiya yahudawan sahayoniyya suka kai kan garin Abba na Lebanon.
Kamarorin matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida sun dauki hotunan jirajen sama marasa matuka ciki na ‘yan gwagwarmaya a lokacin da suke ratsa sararin samaniyar garin Akka da aka mamaye, inda suka isa cibiyar hedkwatar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila tare da mata luguden wuta.