Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne.
Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda zasu nunasu nan ba da dadewa ba. Sannan ya kara da cewa dukkan jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aiki na zama, wanda sabbin jiragen saman yakin da ake kerasu a wasu kasashen basu yi gaba da su a wani daga cikin a kayakin aiki na zamani ba.
Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ya nakalto babban kwamnadan sojojin sama na JMI Bugedia Janara Hamid wahidi yana fadar haka.
Wahidi ya kammala da cewa sojojin sama na JMI a shirye yake su aiwatar da umurnin babban kwaman dukkan sojojin kasar.