Luguden wutar jiragen saman sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa tare da raunata wasu na daban birnin Khan Yunis da sansanin Jabaliya
Majiyoyin asibitin Falasdinawa sun bayyana cewa: Wasu Falasdinawa hudu sun yi shahada, yayin da wasu suka jikkata da sanyin safiyar yau Lahadi, lokacin da jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai hare-hare kan wasu gidaje biyu a sansanin ‘yan gudun hijira na Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza.
Shafin sadarwa na yanar gizo na “Wafa” ya bayyana cewa: Jami’an bayar da agajin gaggawa da masu aikin ceto sun gano gawarwakin shahidai hudu da wasu da dama da suka samu raunuka da suka hada da kananan yara da mata a karkashin baraguzan gidaje guda biyu da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi musu luguden bama-bamai a kan Titin Al-Hoja da ke sansanin Jabaliya.
Yayin da wata mata da yaro guda sun yi shahada wasu kuma suka jikkata a lokacin da jirgin saman sojin mamayar yahudawan sahayoniyya suka kai harin bam a wani gida na iyalan Musabeh a garin Abasan Al Kabira da ke gabashin Khan Yunis a kudancin Zirin Gaza.