Jiragen Saman Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Luguden Wuta Kan Asibitin Baptist Da Ke Gaza

Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa Wakilin

Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa

Wakilin gidan talabijin na Al-Alam Mohammed Al-Balbisi ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu gine-gine na asibitin Baptist, da suka hada da ginin sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa da kuma motocin daukar marasa lafiya da wasu sassa da tantuna da ke ba da hidima ga wadanda suka jikkata.

Ya yi nuni da cewa da sanyin Safiya yau Lahadi, sojojin mamayar Isra’ila sun harba makamai masu linzami da dama kan wadannan gine-gine lamarin da ya tilastawa marasa lafiya da likitoci ficewa daga asibitin tare da fakewa a nesa da asibitin, inda hare-haren suka rusa gine-ginen asibitin.

Wakilin ya kara da cewa: Wannan shi ne karo na biyu da ake kai wa asibitin Arab Baptist hari, domin an kai harin bama-bamai a farkon fara kai hari kan Gaza, wanda ya yi sanadin mummunan kisan kiyashi da ya ci rayukan daruruwan mutane.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments