Iran: Jagora Ya Ce Hajjin Bana Hajjin Bara’a Ne Daga Makiya, HKI Da Masu Goya Mata Baya

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’ee ya bayyana cewa hajjin bana, hajji ne na musamman, banda tsarkake niyya

Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamina’ee ya bayyana cewa hajjin bana, hajji ne na musamman, banda tsarkake niyya ga All…kuma hajji ne na nuna bara’a da kubuta daga makiya, wadanda kuma sune HKI da magoya bayanta.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jagoran yana fadar haka a safiyar yau Litinin a lokacinda yake ganawa da jami’an hukumar mahajjata na kasa da wasu maniyyata a hajjin bana a gidansa a nan Tehran.

Jagoran ya kara da cewa har’ila yau hajjin bana hajji ne na hadin kai tsakanin musulmi a duniya don ta hanyar hadin kai ne musulmi zasu sami karfi a duniya.

Ya ce, akwai wasu al-amura sai a Hajj za’a samesu don haka maniyya kada su yi wasa da su, kuma sun hada da dakin Kaaba, Masallacin Harami, ziyarar manzon All..(s) da wasu wurare masu tsarki wadanda sai a kasa mai tsarki ake samunsu.

Ya kamala da cewa, kayakin kasuwanci ana samunsu a ko ina a duniya, don haka kada mahajjata su maida hankali sosai da yawon saye saye, duk da cewa shi ma yana da kyau.

Daga karshen ya bayyana cewa haduwa da sauran musulmi a duniya yana daga cikin manufofin aikin hajji, don a nan ne masulmi zasu san juna su kuma dauki mataki guda don warware matsalolinsu. Sannan su tattauna dangane da yada addinin musulunci a sauran kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments