Falasdinawa fiye da 20 ne suka yi shahada da suka hada da kananan yara a farmakin da sojojin yahudawan sahayoniyya suka kai kan gidaje a birnin Rafah
Rahotonni sun bayyana cewa; Akalla Falasdinawa 21 ne suka yi shahada da suka hada da kananan yara sakamakon hare-haren wuce gona da iri da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan gidajen fararen hula a birnin Rafah daga yammacin jiya Lahadi zuwa wayewar garin yau Litinin.
Rundunar tsaron farar hula ta Falasdinu ta yi nuni da cewa: Har yanzu ma’aikatan tsaron fararen hula a birnin Rafah na ci gaba da fuskantar masifar hare-haren yahudawan sahayoniyya kan gidajen fararen hula, wadanda suka yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da jikkata wasu da kuma bacewar wasu a karkashin baraguzan gine-gine.