Search
Close this search box.

Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Jaddada Wajabcin Daukan Kwakkwaran Mataki Kan H.K.Isra’ila

Ministan harkokin wajen Iran ya ce: Dole ne a dauki matakin dakatar da yahudawan sahayoniyya daga kashe yara da hukunta su kan hakan Ministan harkokin

Ministan harkokin wajen Iran ya ce: Dole ne a dauki matakin dakatar da yahudawan sahayoniyya daga kashe yara da hukunta su kan hakan

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussein Amir Abdul-Ilahiyon ya jaddada cewa: Duk wani salo da ingantacciyar rawar da gwamnatocin kasashen musulmi za su taka wajen tunkarar yakin Gaza, za su kasance cikin tarihi, kuma yanke huldar diflomasiyya da tattalin arziki da kuma haramcin sayar da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna daga cikin muhimman matakan mayar da martani kan yakin Gaza gami da tilasta kawo karshen kisan kiyashi kan Falasdinawa da hana aiwatar da laifukan cin zarafi a yankunan Gabar yamma da kogin Jordan da birnin Qudus mai alfarma. A jawabin da ya gabatar a wajen taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi karo na 15, wanda aka gudanar a karkashin taken “Karfafa hadin kai da kusanci ta hanyar tattaunawa don samun ci gaba mai dorewa” a birnin Banjul fadar mulkin kasar Gambiya, Hussain Abdul-Ilahiyon ya yi Allah wadai da ci gaba da aikata munanan laifuka  da yahudawan sahayoniya suke yi kan al’ummar Gaza tare da jaddada

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments