Jigo A Kungiyar Hamas Mustafa Abu Ara ya yi shahada a gidan kason Isra’ila

Hukumar kula da harkokin fursunonin Palastinu da kungiyar fursunonin Falasdinu sun tabbatar da cewa Sheikh Mustafa Abu Arra mai shekaru 63 da haihuwa wanda ake

Hukumar kula da harkokin fursunonin Palastinu da kungiyar fursunonin Falasdinu sun tabbatar da cewa Sheikh Mustafa Abu Arra mai shekaru 63 da haihuwa wanda ake tsare da shi a gidan kason Isra’ila ya yi shahada, bayan an dauke shi daga gidan kason “Ramon” na Isra’ila zuwa asibitin “Soroka” sakamakon mummunan yanayin da yake ciki na tabarbarewar lafiyarsa.

Cibiyoyin Palasdinawa biyu masu mayar da hankali kan harkokin fursunoni a cikin wata sanarwa da suka fitar sun bayyana cewa, Sheikh Mustafa Abu Arra, daga garin Aqqaba da ke gundumar Tubas a yammacin gabar kogin Jordan, babban  jigo ne a kungiyar Hamas, kuma ya shafe tsawon lokaci ana tsare da shi a gidajen yarin Isra’ila. An kama shi sau da yawa tun 1990, wanda Isra’ila ta kama shi tare da tsare day a kai tsawon kusan shekaru 12.

Yana daga cikin Falastinawa ‘yan gudun hijira da Isra’ila ta kora daga Marj al-Zuhour da ke kudancin kasar Lebanon a shekara ta 1992. Sojojin mamaya sun sake kama shi a ranar 30 ga watan Oktoban 2023, duk kuwa da mummunar rashin lafiya da yake fama da ita, da kuma bukatar  kulawar likitoci tun kafin a kama shi.

Hukumar da ke kula da fursunoni ta jaddada cewa Sheikh Abu Arra, kamar sauran fursunoni, ya fuskanci muzgunawa da azabtarwa da yunwa, da kuma rashin bashi damar samun kulawar likitoci, wadanda su ne manyan abubuwan da suka haifar da shahadar fursunoni da dama a gidajen yari da sansanonin mamayar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments