Jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Sojojin Yemen sun harba makamai masu linzami sama da 200 kan haramtacciyar kasar Isra’ila
Jaridar Ma’ariv ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana cewa: Dakarun kungiyar Ansarullah ta Yemen da hadin gwiwar sojojin kasar sun harba makamai masu linzami sama da 200 da jiragen sama marasa matuka ciki fiye 170 kan haramtacciyar kasar Isra’ila tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023.
Ma’ariv ta yi da’awar cewa: Amurkawa da sojojin sama da na ruwa na haramtacciyar kasar Isra’ila sun kakkabo akasarin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki da aka harba daga Yemen.
Tun da farko a yau Asabar, mai magana da yawun sojojin mamayaryahudawan sahayoniyya ya sanar a cikin wani takaitaccen bayani a shafin dandalin “X” Bayan harba makami mai linzami daga Yemen da safiyar yau Asabar da kuma kunna kararrawar gargadi a tsakiyar haramtacciyar kasar Isra’ila kan yahudawan sahayoniyya su shige maboyar karkashin kasa, kuma an yi yunkurin kakkabo makaman mai linzami amma ba a yi nasara ba.
Bugu da kari, hukumar kula da motocin daukar marasa lafiya ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta ce: Mutane 18 ne suka jikkata sakamakon fadowar makamin mai linzami na Yemen a yankin mafi girma na birnin Tel Aviv fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra’ila da safiyar yau Asabar.