A wani rahoton musamman da jaridar ” Telegraph” ta Birtaniya ta buga, ta amabci cewa; makamai masu linzami da Iran ta harba wa Isra’ila sun sauka kai tsaye akan wasu muhimman cibiyoyin soja.
Jaridar ta kara da cewa; Mahukuntan Isra’ila ba su bayyana wa duniya wadannan wuraren da makamai masu linzamin su ka fadawa ba, saboda aiki da dokar soja ta Sakaye labaran wuraren da aka kai wa hare-hare.
Rahoton jaridar ya ce, ya sami bayanai ne daga hotunan tauraron dan’adam na jamiar Jahar Oregon da suka saba yin aiki da irin wadannan bayana da suke tarawa domin gano barnar da aka yi a wuraren yaki.
Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyoyin sojan da Iran ta kai wa harin, a baya ba a yi Magana akansu ba, sai yanzu kuma suna a cikin yankunan arewa, kudanci da tsakiyar ne. Daga cikin wuraren da akwai sansanin sojan sama mafi girma, cibiyar tattara bayanai na sirri, da kuma wata cibiya ta ajiyar kayan yaki.
A jiya juma’a sojojin HKI sun ki amsa tambayar jaridar ta Telegraph akan zurfin asarar da hare-haren na Iran su ka yi wa cibiyoyin nasu.
Sai dai kuma jaridar ta ce, wadannan sabbin cibiyoyin sojan da ake Magana makamai masu linzami na Iran sun suka a cikinsu,kari ne akan wasu 36 da Iran din kai wa farmaki, wadanda na’urorin da HKI take takama da su na kakkabo makamai, su ka kasa tare su, kuma sun yi barna mai girman gaske.