Search
Close this search box.

Jamus: Makiya Musulmi Da Musulunci Suna Kara Takurawa Musulmi A Kasar Jamus

Kafafen yada labaran kasar Jamus sun nakalto wata majiyar gwamnatin kasar na cewa: yawan musulmi wadanda ake cutar da su a kasar yana karuwa idan

Kafafen yada labaran kasar Jamus sun nakalto wata majiyar gwamnatin kasar na cewa: yawan musulmi wadanda ake cutar da su a kasar yana karuwa idan an kwatanta da shekara ta 2023 da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran DPI na kasar ta Jamus ya nakalto Christophe de Vries wani lauyan jam’iyyar ‘Christian Democrat Union’ (CDU) yana cewa a binciken da ya gudanar ya gano cewa yawan musulmi da aka cutar a kasar Jamus a shekara ta 2023 sun kai 1,610, wanda idan an kwatanta da shekarar da ta gabata adadin ya karu da 610. Sannan yansanda a kasar Ta Jamus sun yi rubuta ayyukan cutar da musulmi a kasar har 137 a cikin watanni uku na farko a wannan shekarar da muke ciki. Banda haka rahoton ya ce karuwar cutar da musulmi a kasar ta Jamus yana da dangantaka da yakin da ke faruwa a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments