Search
Close this search box.

Jami’in Yahudawa Ya Yi Furuci Da Cewa Yaki Ba Zai ‘Yantar Da Fursunonin Yahudawa Ba

Wani jami’in haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ba zata cimma manufofinta na yaki a Gaza ba Tashar talabijin ta 13 ta haramtacciyar

Wani jami’in haramtacciyar kasar Isra’ila ya ce: Gwamnatin yahudawan sahayoniyya ba zata cimma manufofinta na yaki a Gaza ba

Tashar talabijin ta 13 ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta nakalto shugaban kwamitin tsaron kasar yahudawan sahayoniyya Tzachi Hanegbi cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba zata cimma ko da daya daga cikin manufofin yakin da take yi a Zirin Gaza ba.

Ya kara da cewa: Ba zai yiwu mu kawar da kungiyar Hamas ba, kuma ba mu cika sharuddan dawo da fursunoninmu ba, kuma ba mu samar da hanyar komar da yahudawan sahayoniyya’yan kaka gida komawa matsuguninsu na Ghalaf Gaza ba cikin aminci.

Ya ce rundunar sojin haramtacciyar kasar Isra’ila da kanta ta yifuruci da cewa: Cimma manufifin yaki kan Gaza yana bukatar shekaru da dama ba shekara daya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments